10 Yuli 2020 - 14:19
Hukumar Lafiya Ta Duniya WHO Ta Yi Gargadin Cewa; Cutar Corona Tana Son Fin Karfin Yadda Ake Yaki Da Ita

Hukumar lafiyar ta duniyar ta kafa wani kwamiti wanda zai binciki yadda take fada da cutar, haka nan ma sauran gwamnatocin duniya, tare da yin gargadin cewa fada da cutar yana son ya ta’azzara.

(ABNA24.com)  Gargadin na hukumar lafiya ta duniya, yana zuwa ne adaidai lokacin da wadanda su ka kamu da cutar corona a fadin duniya yah aura miliyan 12

Shugaban hukumar lafiyar ta duniya Adhanom Ghebreyesus ya ce; cutar ta Covid-19 wacce kusan kowane mutum guda a duniyar nan ya tasirantu da ita, ta cancanci a sake yin nazari mai tsafta akan yadda ake fada da ita.

Adhanom Ghebreyesus ya kara da cewa; A kowace rana ta Allah cutar sai kara muni take yi, kuma ta fi karfin a shawo kanta a cikin yankuna mafi yawa na duniya.

Shugaban hukumar kiwon lafiyar ta duniya ya kara da cewa; Babu yadda za yi mu iya samun galaba akan cutar matukar kawukanmu suna ci gaba da rarraba, yana mai karawa da yin gargadin cewa; sabanin da ake da shi a tsakanin kasashe a duniya yana taimakawa wajen kara yaduwar cutar.

342/